An bukaci alummar Kano da gwamnatoci dasu shigo harkar Ilimin kimiyya domin agazawa masu karamin karfi musamman mata.
Ajiyan Gaya Alhaji Shamsu kademi ya bukaci haka lokacin bikin bude fannin karatun digiri na makarantar Emirate College of Health Science dake Kabuga.
Gwamna Yahaya Bello ya kyautarwa da Tinubu ofishin yakin neman zaben sa
Hakimin yakara da cewar akwai masu karamin karfin da basa iya daukar nauyin karatun ‘ya’yansu Amma Kuma suna da kwakwalwar fahimtar karatun inda yace samarwa mata Ilimin kimiyya zai taimaka wajan yawaitarsu a Asibitoci domin sudinga duba ‘Yan uwansu mata.
Shima a nasa jawabin Daraktan makarantar wato Dr.Sulaiman Shuaibu ya ce sunyi nasarar Hada Kai da jami’ar Jihar Kwara wajan Fara karatun Digiri a wasu fannoni musamman na kimiyya hakan yasa yau suka Rantsar da dalibai tamanin da bakwai wadan zasu Fara wannan karatun.