[HOTUNA]: Yadda ƴan majalisar Shura ta Shekarau su ka raba Naira miliyan 100 da Atiku ya basu

0
76
Wasu hotuna sun nuna wasu mambobin Shura, majalisar shawara ta harkar siyasar Sanata Ibrahim Shekarau, suna raba wani kaso na Naira miliyan 100 da ake zargin ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayar domin tara magoya bayan jam’iyyar a ziyarar da ya kai Kano.
Wasu majiyoyi sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa ɗan takarar shugaban ƙasa ya yiwa shugabannin PDP na Kano wanka da kuɗi har naira miliyan 130, inda Malam Shekarau ya samu kaso mafi tsoka na Naira miliyan 100, shi kuma ɓangaren Aminu Wali ya samu Naira miliyan 30.
Sai dai wata majiya ta ce hotunan ba na rabon miliyan N100 da Atikun ya bayar ba ne, na rabon tallafin miliyan N50 da miliyan N10 da ya ba wa ‘yan kasuwar Kantin Kwari da Beirut Road wadanda ibtilain ambaliyar ruwa da rushewar gini ya shafa.
A karshen watan Agusta ke dai Atiku ya ziyarci Kano domin karɓar Malam Shekarau, wanda ya sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP ta Rabiu Kwankwaso zuwa PDP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here