Lewandowski zai fuskanci Bayern Munich

0
99

Kociyan Bayern Munich, Julian Nagelsmann ya ce ya kagu ya sake haduwa da Robert Lewandowski, bayan da za su fafata da Barcelona a Champions League.

Kungiyoyin biyu za su fafata a gasar Zakarun Turai ranar Talata wasa na biyu a rukuni na uku.

Ranar 7 ga watan Satumba, Bayern Munich ta je Italiya ta doke Inter Milan da ci 2-0 a wasan farko a rukuni na ukun.

Ita kuwa Barcelona a Camp Nou ta ci FC Viktoria Plzen 5-1, kuma Robert Lewandowski ne ya ci mata uku a karawar.