Majalisar dokokin Kano ta nemi ƴan majalisar tarayya su dauki matakin da ya dace kan dam din Tiga

0
124

Majalisar dokokin jihar Kano, ta buƙaci ƴan majalisar tarayya da ke wakiltar Kano da su yi gaggawar yin kira ga gwamnatin tarayya don dauki matakin da ya dace kan dam Tiga domin ceto rayuka da dukiyoyin mazauna yankin.

Hakan dai ya biyo bayan ƙudurin haɗin gwiwa da dan majalisar Ƙiru kuma mataimakin shugaban majalisar Kabiru Hassan Dashi da na Bebeji Abubakar Uba Galadima da wakilin Rano Nuruddeen Alhassan Ahmad suka gabatar.

Da yake gabatar da ƙudurin, Alhaji Kabiru Hassan Dashi, ya ce, akwai buƙatar ɗaukar matakin gaggawa kan madatsar ruwan ta Tiga tun kafin ta haifar da mummunar ɓarna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here