‘Yan sanda sun kama wata budurwa kan zarginta shekawa wani saurayi ruwan shayi

0
74

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sami nasarar cafke wata budurwa wadda ake zarginta da laifin shekawa wani saurayi ruwan Shayi a jikinsa.

Mai magana da yawun rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a Kano.

Haruna Kiyawa yace, lamarin ya faru ne a unguwar Rimin Auzunawa, inda Maryam Haruna ta kona Lawan Inuwa da ruwan zafi na Shayi, bayan sun sami korafin ne rundunar ta aike da jami’anta zuwa gurin inda suka dauki matashin kuma suka garzaya dashi zuwa Asibiti domin ceto lafiyarsa.

Budurwar mai suna Maryam Haruna da ake zargi da laifin kona saurayin Lawan Inuwa dai,tace sun sami sabani dashi ne kuma tsautsayi yasa ta dakko ruwan shayi ra sheka masa jiki.

Rundunar ‘yan sandan ta gargadi mutane dasu kaucewa daukar doka a hannu musanman domin gujewa fadawa tarkon dana sani.