An dakatar da shugaban Zimbabwe halartar taron binne Gawar Elizabeth ta II

0
71

Sarkin Ingila Charles na III ya dakatar da bukatar shugaban Kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa Halartar babban taron binne Gawar Marigayiya sarauniyar Ingila Elizabeth ta ll .

An shirya taron binne ta ne ranar litinin 19 ga watan Satimbar na 2022.

Tunda farko a takardar sakon ta’aziyya da ya aikewa Sabon Sarkin na Ingila, shugaban Zimbabwe Emmerson ya nemi a bashi dama yaje Fadar ta Buckingham domin ya halarci taron binne Elizabeth din ,duk dacewa baya cikin Shugabanin duniya da aka gayyata .

A takardar martin da Fadar Buckingham ta mayar masa ta hannun babbar Mataimakiya a bangaren yada labarai Dake fadar Sarkin na Ingila Miss Jennie Vine tace Sarki Charles na III bai amince da bukatar shugaban na Zimbabwe ba saboda zarginsa da keta bakin Dan Adam a kasarsa.

Takardar ta Kara dacewa sakamakon dokokin da aka saka na takaita zuwa binne Gawar Marigayiya Queen Elizabeth ta ll musamman a bangaren tsaro ba zaiyiyu a bar shugaban na Zimbabwe yaje Birtaniya ba saboda akwai Yan kasarsa da suke zaune a can Dan gudun kada ana alhini wasu su tada bore idan sunga shugaban na Zimbabwe a can.