ADC ta kori ɗan takararta na shugaban ƙasa

0
64

Gabanin zaben 2023, jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta kori dan takararta na shugaban kasa, Mista Dumebi Kachikwu daga jam’iyyar.

A makon da ya gabata ne dai jam’iyar ta dakatar da Kachikwu bisa wasu zarge-zarge.

Sai dai a yau Asabar, shugaban jam’iyyar na kasa, Ralphs Nwosu a wata sanarwa da ya fitar ya ce an kori Kachikwu ne saboda wasu abubuwa na zagon-ƙasa ga kundin tsarin jam’iyyar.

Ya ce kwamitin mutum bakwai da jam’iyyar ta kafa wanda ya shafe kwanaki shida yana aiki, ya mika rahotonsa a ranar Alhamis.

Nwosu ya ce a ranar Juma’a ne kwamitin ayyuka na jam’iyyar (NWC) ya tattauna kan rahoton tare da karɓar rahoton kwamitin tare da gyara a kai.

Sauran mutanen da aka kora daga jam’iyyar sun haɗa da Kennedy Odion, Kingsley Oggah, Musa Hassan, Bello Isiyaka, Clement Ehiator, Kabiru Hussaini da Alaka Godwin.