Wani dan Chana ya kashe budurwarsa a Kano

0
213

Rahotanni na nunar da cewa al’ummar Janbulo sun kwana cikin alhini da fargaba, bisa Zargin wani dan kasar Chana da halaka wata budurwa Mufeeda ta hanyar chaka mata wuka.

Lamarin ya faru ne a cikin daren jiya Juma’a, inda wanda ake zargi dan asalin kasar Sin ya garzaya har inda margayiyar take a unguwar Jan Bululo dake Kano tare da kashe ta.

Sai dai bayan da al’ummar unguwar suka fito da nufin daukar fansa, jami’an ‘yan sanda sunyi nasarar kubutar da shi tare da wucewa da shi ofishin su.

Kawo yanzu ‘yan sanda basuyi karin bayani ba.