HomeLabaraiBirtaniya: ’Yan Najeriya 56 sun mutu sun bar dukiya babu magada

Birtaniya: ’Yan Najeriya 56 sun mutu sun bar dukiya babu magada

Date:

Related stories

Hukumar DSS ta kama wasu bata gari da ke sayar da sabbin takardun kudi na Naira

Ma’aikatar harkokin wajen kasar a ranar Litinin din nan...

Yadda lamari ya kasance yayin zuwan Buhari Kano don kaddamar da aiyuka 8

An tsauraran matakan tsaro a cikin birnin Kano da...

Najeriya ta yi asarar likitoci 2800 a cikin shekaru biyu – NARD

Shugaban kungiyar likitocin Najeriya NARD, Dr Innocent Orji ya...

Yadda ake canzar da kudin Sepa zuwa Naira a yau Litinin

Farashin Separ Nijar zuwa Naira a farashin kasuwar canjin...

Gwamnatin Birtaniya ta wallafa jerin sunayen ‘yan Najeriya 56 da suka mutu suka bar dukiya mai tarin yawa a kasar amma ba tare da an gano makusanta da za su gaji wannan dukiyar ba.

An ruwaito cewa, daga cikin dukiyoyin da mutanen suka mutu suka bari har da gidaje, wadanda a karkashin dokokin Birtaniya, matukar aka share tsawon shekaru 30 daga ranar mai ita ya mutu amma ba a gano magadan mamancinsa ba, dukiyar za ta zama mallakin baitil-mali.

Daga cikin mamatan da Gwamnatin Birtaniyar ta fitar da sunayesu kuma aka rasa magadansu  har da wani mai suna Mark N’woko da ya rasu tun ranar 9 ga watan Disambar 1992 a garin Surrey da ke Birtaniya.

Hakazalika, akwai wani mai suna Victor Adedapo Olufemi Fani-Kayode, wanda ya mutu ranar 15 ga watan Agustan 2001 a Biermingham, to amma har yanzu ba wanda ya gabatar da kansa a matsayin dan uwa ko makusanci domin ya gaje shi.

Haka kuma a jerin mamatan, akwai Adenike Adebiyi da ya mutu a 2004; Akanni Jeremiah Adejumo da ya mutu a 2017; Solomon Adekanmibi a 2021; Richard Adesanya a 2011; Jeff Adhekeh a 2021; Isaac Ademola Adio a 2012; Julius Ajidahuan a 2009 da Julius Taiwo Akinyeye dan asalin Jihar Ondo wanda ya mutu a 1995 da sauransu.

Aminiya

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories