Gwamnatin Kano za ta kashe naira biliyan 1.2 wajen sake gina shataletale da hanyoyi 42

0
68

Gwamnatin Jihar Kano za ta kashe naira biliyan 1.2 wajen gina shataletale da gyara hanyoyin cikin gari guda 42 da suka lalace sakamakon mamakon ruwan saman da aka samu a daminar bana.

Kwamishinan yada labaran jihar Malam Muhammad Garba ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar a karshen makonnan.

Ya ce wasu daga cikin shataletalen da za a sake gina sun hada da na gidan man A A Rano dana First Bank da makamantansu.

Malam Muhammad Garba ya ce wasu daga cikin hanyoyin cikin garin da za a gyara sun hada da Titin Audu Bako da na Hotoro Tsamiyar Boka da Kwanar Jaba-Kwana Hudu.

Sai kuma Titin Gwarzo da Sheikh Jafar da Muhammadu Buhari dakuma Sabo Bakin Zuwo da sauransu.

Ya kara dacewa tuni aka kafa wani kwamatin kwararru na injiniyoyi da suka fito daga ma’aikatar ayyuka da tsara birane dakuma wasu ma’aikatu da hukumomi domin gudanar da wannan aiki.

Kwamishin ya kara dacewa tuni kwamatin ya tuntubi wasu daga cikin kamfanonin da za su yi wannan aiki.