Rundunar sojin sama ta sake kai wa Turji farmaki

0
45

Wani jirgin yaki na rundunar sojojin saman Najeriya, NAF ya kaddamar da wani sabon hari a maɓoyar shugaban ƴan bindigar Zamfara, Bello Turji.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, dan bindigan, wanda ya yi kaurin suna ya tsallake rijiya da baya a wani harin bam da aka kai masa a gidansa da yammacin ranar Asabar.

Sai dai kuma wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa jirgin yakin ya koma yankin, da misalin karfe tara na safiyar yau Litinin, inda ya jefa bama-bamai a ƙalla biyu.

A halin da ake ciki, wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan sansanin Turji ne sun kai farmaki kan matafiya a kan hanyar Sokoto zuwa Gusau a Shinkafi, da safiyar yau Litinin.

Wani mazaunin garin Shinkafi, Murtala Wadatau, ya ce ‘yan bindigar sun tare hanya a Kwanar Badarawa da Birnin Yero.