Ministan Kwadago Da Daukar Aiki, Chris Ngige, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shawarar karin albashi ga dukkan ma’aikata a Najeriya saboda wahalar rayuwar da ake ciki a fadin kasar.
Ngige ya bayyana hakan yayinda ya gabatar da jawabi a taron kaddamar da littafin cikar kungiyar kwadagon Najeriya (NLC) shekaru 40 a Abuja, ranar Litinin, rahoton Tribune.
Ministan na kwadago ya ce kara albashin ya zama wajibi saboda halin matsin tattalin arziki da ake fama a fadin duniya, musamman Najeriya.
“Hauhawar tattalin arziki ta shafa duniya gaba daya, zamu yi karin mafi karancin albashi bisa abubuwan dake faruwa.”
“Mun fara karin da kungiyar malaman jami’a ASUU saboda yanzu suna tattaunawa da ma’aikatar Ilimi.”
Shugaban TUC, Festus Osifo, ya bayyana cewa yan siyasa sun dade suna cin zarafin ma’aikatan Najeriya.
Yace biyan ma’aikata mafi karancin albashin N30,000 ba zai ko kudin mota ba zai isa ba a wata.