Kotu ta umarci ASUU ta janye yajin aiki nan take

0
73

Kotu ta umarci Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) da ta janye yajin aikinta ba tare da bata lokaci ba.

Kotun ma’aikata, ta bayar da umarnin ne a ranar Laraba, bayan malaman jami’ar sun shafe sama da wata bakwai suna gudanar da yajin aiki.

Gwamnatin Tarayya ta maka kungiyar a kotu ne tana bukatar a tilasta wa malaman jami’a komawa bakin aiki, bayan bangarorin biyu sun gaza cim-ma matsaya domin kawo karshen yajin aikin kungiyar.

Lauyan Gwamnatin Tarayya, JUK Igwe, ya bayyana wa kotun cewa bai wa ASUU umarnin na da muhimmaciv, kasancewar kungiyar ta kawo tsaiko ga harkokin karatu da a jami’o’i.