Majalisar wakilai ta kasa tayi Allah wadai da kisan Ummita da wani Dan China yayi a Kano

0
178

Majalisar wakilai ta Najeriya ta bayyana takaici tare da yin Allah wadai da kashe wata yarinya Ummukulsum Sani Buhari da wani Dan kasar Sin yayi a karshen makon daya gabata.

Majalisar tayi Allah wadai da lamarin ne Sakamakon kudirin gaggawa da Wakilin Kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure a majalisar Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum yayi inda ya bayyana kisan a matsayin na zalinci Kuma Wanda ya Saba doka.

A yayin Dayake gabatar da kudirin Turakin na Rano ya bukaci majalisar ta yi Kira ga hukumomin tsaro su gudanar da kwakwkwaran bincike su Kuma gurfanar da Wanda ake zargin a gaban kotu Dan ya girbi abinda ya shuka.

Ya Kuma bukaci ‘Yan majalisar dasu tashi tsayi ayi shiru na Minti daya da zummar yin Addua ga marigayiyar tare da bukatar a kafa kwamitin da zai ziyarci Jihar Kanon da lamarin ya faru Dan jajantawa iyaye da ‘yan uwan Yarinyar dama Gwamnatin jihar baki daya.

Kudirin dai ya samu cikakken goyon baya ga daukacin ‘yan majalisar da suka halacci zaman in Banda wani Dan majalisar dake wakiltar wata mazaba a cikin Birnin Kano Wanda ya nuna rashin goyon bayansa tare da cewar Bai maga dalilin kawo wannan kudiri ba.

Tuni dai kudirin ya samu karbuwa Kuma majalisar ta amince da bukatu da Wakilin Kananan hukumomin na Rano, Kibiya da Bunkure Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum ya gabatar cikin kudirin nasa.

A ranar Asabar data gabata ne dai wani Dan kasar China mazaunin Jihar Kano Geng Quarong ya haura har gidan su wata yarinya Budurwarsa Ummita dake Unguwar Jan bulo ya caccaka mata Wuka har ta mutu sakamakon kin karbar bukatar autensa da ta.