Barkewar cutar amai da gudawa ta kashe mutum 10 a Gombe

0
77

Hukumomi a jihar Gombe sun ayyana barkewar cutar amai da gudawa ta kwalara bayan da mutum 10 suka hallaka ta sanadin cutar.

Da yake zantawa da kamfanin dillacin labaran Najeriya a yau, kwamishinan lafiya na jihar Gombe, Habu Dahiru ya bayyana yadda cutar ta tunbatsa a Gombe.

Dahiru, wanda sakataren hukumar lafiya ta matakin farko, Abdulrahman Shuaibu ya wakilta ya ce, a ranar 20 ga watan Satumba kadan mutum 236 ne suka kama da cutar a Gombe.

A cewarsa; “A wannan shekarar, daga watan Yuni an gano adadi mai yawa na wadanda suka kamu da cutar kwalara a karamar hukumar Balanga kuma saboda shiri da kuma daukar matakin gaggawa, an samu nasarar shawo kan lamarin.

“Cutar ta barke ne unguwanni takwas na kananan hukumomin Balanga, Yamaltu-Deba, Nafada, Funakaye da Gombe a fadin jihar.

“Hukumar lafiya ta jihar Gombe ta gaggauta kawo hanyar daukar mataki da dakilewa har ma da kula da cutar. “Ya zuwa 20 ga watan Satumba, akwai kari matuka a adadin wadanda suka kamu da cutar, domin akalla mutum 236 ne aka gano suna dauke cutar a fadin jihar Gombe.”