Makashin Ummita zai riƙa cin abincin ƙasarsu ne ba gabza ba – Gidan yari

0
113

Hukumar Kula da Gidan Gyaran Hali ta Ƙasa ta bayyana cewa Geng Quanrong, wanda ake tuhuma da kashe budurwarsa, Ummukulthum Buhari a nan Kano, zai riƙa cin irin abincin ƙasarsu ne ba wai gabza ba.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, a jiya Laraba ne Kotun Majistire mai lamba 30 da ke zaman ta a Titin Zungura a Kano ta aike da Quanrong zuwa gidan yari, bayan da ta tuhume shi da kisan kai.

Alƙalin kotun, Hanif Sanusi Yusuf ya ce laifin ya saɓa da sashi na 221 na kundin laifuka, inda ya ɗage zaman kotun zuwa 13 ga watan Oktoba, ya kuma bada umarnin da a ajiye shi a gidan gyaran hali.

Sai dai kuma da ya ke ƙarin haske a kan ko ya zaman Quanrong a gidan yarin, Kakakin Hukumar Kula da Gidan Gyaran Hali a Kano, DSC Musbahu Lawal Kofar Nasarawa ya shaida wa Freedom Radio cewa abincin ƴan China zai riƙa ci.

A cewar Kofar Nassarawa, jama’a na ta tambayar ko wanne irin abinci za a riƙa bai wa wanda ake zargin.

Ya yi bayani cewa doka ta bada damar a rika baiwa fursuna, wanda ba ɗan ƙasa ba kula wa ta musamman, wato “special treatment”, inda ya ƙara da cewa “za a riƙa bashi irin abincin ƙasarsu ne ba gabza ba.”

Ya ƙara da cewa doka ma ta bada damar ya sanar da ofishin jakadancin ƙasar sa ko kuma ƴan uwansa da za su iya taimaka masa.

(DAILYNIGERIA)