Sojoji sun hallaka ’Yan Boko Haram 7 a Borno

0
143

Sojojin Najeriya karkashin rundunar tsaro ta Operation Hadin Kai sun yi wa wasu ’yan ta’addan Boko Haram kwanton-bauna a karamar hukumar Jere da ke jihar Borno, inda suka kashe bakwai daga cikinsu.

Rahotanni sun ce a sakamakon harin wanda aka kai kauyen Kayamla na karamar hukumar, an kuma kama kayayyaki da dama daga hannun ’yan ta’addan, yayin da wasu daga cikinsu suka gudu da raunuka a jikinsu.

Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa nasarar sojojin a biyo bayan samun wasu bayanan sirrin da suka kai ga hallaka mayakan.

“Dakarun rundunar tsaro ta Operations Hadin Kai sun kashe ’ya ta’adda bakwai yayin wani kwanton-bauna, wasu kuma sun gudu da raunuka a jikinsu a kauyen Kayamla,” inji majiyar.

Da yake tabbatar da labarin, wani masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce lamarin ya ritsa da su ne lokacin da suke kokarin gujewa munanan hare-haren sojoji a maboyarsu.

Bayanai sun ce dakarun bataliya ta 73 da hadin gwiwar rundunar CJTF ne suka gudanar da hare-haren.

Majiyoyi sun ce ’yan ta’addan kan je yankin don kai wa manoma hare-hare sannan su sace wau mazauna yankin.

Zagazola Makama ya ce a ’yan kwanakin nan sojojin sun dada zafafa kai hare-hare a kan ’yan ta’addan, masu samar musu da bayanai da kuma masu kai musu kayan aiki.