‘Yan bindiga sun kai sabon hari Abuja

0
68

Mutum biyar maza hudu da wata matar aure sun nuste a garin tserewa harin ‘yan bindiga a kauyen Chakumi a unguwar Gurdi ta Abaji a Abuja.

Chakumi gari ne mai makwabtaka da kauyen Daku mai hade da kogin Gurara a unguwar Dobi ta Gwagwalada a birnin na Abuja.

Mai garin Chakumi, Mohammed Magaji ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce hakan ya faru ne da misalin karfe 11 na safe a ranar Laraba 21 ga watan Satumba.

Ya kara da cewa, wadanda suka mutun, ciki har da matar aure mai kananan shekaru na aiki ne a gona lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari.

Ya ce da ganin ‘yan bindigan, sun gaggauta hawa kwale-kwale domin tserewa zuwa kauyen Dakuke, amma hakan ya zama sanadi suka rasa rayukansu a kogin na Gurara.

A cewarsa: “Ko yanzu da muke magana, ba a ciro gawarwakin mutanen da suka mutun ba saboda masunta daga Daku da kuma kauye na ci gaba da neman gawarwakin.

” Mai garin ya koka da yadda ‘yan bindiga suka addabi yankin, ya kuma ce manoma sun daina zuwa gonakinsu saboda tsoron ta’addancin ‘yan bindiga.

Mataimakin shugaban karamar hukumar Abaji, Ibrahim Abubakar ya tabbatar da lamarin, ya kuma ce daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa dasu danginsa ne.