Yawan gutsuri tsoma da rashin tabbas ya tilastawa Jam’iyar PDP Kiran taron gaggawa

0
76

Babbar Jam’iyar Adawa ta PDP a Najeriya ta Kira taron gaggawar Jim kadan bayan da tawagar Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike da na jihar Oyo Seyi Makinde da tsohon Ministan yada Labarai Farfesa Jerry Gana da wasu daga cikin jiga jigan Jam’iyar PDPn suka janye jiki daga kwamitin yakin Neman zaben ATIKU Abubakar.

Gwamna Wike da tawagar tasa sun sanar da matsayar tasu ne a lokacin da ake shirye shiryen kaddamar da kwamitin yakin Neman zaben ATIKU a ranar Laraba Mai zuwa.

Jaridar Hausa 24 ta rawaito cewa tunda Farko Wike yace muddin baa sauke shugaban PDP na kasa Ayu ba to ba zasuci gaba da zama inuwa Daya da su ATIKU ba .

Mai magana da yawun Jam’iyar PDP na kasa Debo Ologunagba ya shaidawa Jaridar Punch cewa tun lokacin da Wike da mutanansa suka janye jiki daga kwamitin yakin Neman zaben ATIKU Abubakar suke taron gaggawa Dan dinke wannan baraka wacce tafi ta baya da suka fuskanta daga bangaren na Wike .

Saidai wata majiya tace Atiku Abubakar ya magantu kan bukatar su Wike na Neman sauke shugaban PDP na kasa Iyochia Ayu Inda yace shi a Karan kansa Yana Jin nauyin ya budi Baki yace Ayun ya sauka daga kujerar tasa.