Rashawa ta ta’azzara rashin tsaro a Najeriya – ICPC

0
51

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC a Najeriya, Farfesa Bolaji Owasanoye, yawaitar cin hanci da rashawa ne ke rura wutar matsalar rashin tsaro a Najeriya.

Farfesan ya bayyana haka ne a yayin da aka fara taron yini biyu na kwamitin majalisar wakilan Najeriya kan yaki da cin hanci da rashawa da cibiyar nazarin harkokin dokoki da dimokaradiyya ta Najeriyar jiya Alhamis a Abuja.

Owasanoye ya zargi wasu ‘yan majalisar dokokin Najeriya da manyan hafsoshin soji da hannu a matsalar ta cin hanci da rashawa, tare da bukatar su kaurace wa laifukan da ke haifar da matsalolin tsaro.

Sata da manyan jami’a ke yi ya lalata rundunar sojin kasar, ya kuma raunana karfin gwiwar dakarun da ke fagen daga, tare da tsawaita yakin da ake da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga.

Mai bai wa shugaban kasa shawara a fannin tsaro, Babagana munguno ya taba korafi a bainar jama’a cewa sun gaza yin bayani a kan kudaden da aka fidda don sayen makamai a lokacin manyan hafsan hafsoshin sojin da suka gabata.

RFI