HomeLabaraiSabon harin sojin sama ya kashe 'yan bindiga 45 a Zamfara da...

Sabon harin sojin sama ya kashe ‘yan bindiga 45 a Zamfara da Katsina

Date:

Related stories

Hukumar DSS ta kama wasu bata gari da ke sayar da sabbin takardun kudi na Naira

Ma’aikatar harkokin wajen kasar a ranar Litinin din nan...

Yadda lamari ya kasance yayin zuwan Buhari Kano don kaddamar da aiyuka 8

An tsauraran matakan tsaro a cikin birnin Kano da...

Najeriya ta yi asarar likitoci 2800 a cikin shekaru biyu – NARD

Shugaban kungiyar likitocin Najeriya NARD, Dr Innocent Orji ya...

Yadda ake canzar da kudin Sepa zuwa Naira a yau Litinin

Farashin Separ Nijar zuwa Naira a farashin kasuwar canjin...

Wani lugeden wutar sojin saman Najeriya ya kashe ‘yan bindiga 45 ciki har da jagoransu Dogo Rabe yayin wani sumame da dakarun suka kai maboyar ‘yan ta’addan a dazukan jihohin Zamfara da Katsina na arewacin kasar.

Luguden Sojin saman Najeriyar a dazukan Zurmi da Birnin Magaji da kuma Jibia wanda ya kai ga mutuwar Dogo Rabe na zuwa kasa da kwanaki 4 bayan makamancinsa da dakarun suka kai maboyar Bello Turji da ya kai ga kisan ‘yan bindiga 22 ko da ya ke bayanai sun ce Turji ya tsere.

Yayin zantawar wani dan jaridar yankin Abdulbaqi Aliyu da jaridar Premium Times ya yi ikirarin cewa harin sojin ya kashe ‘yan bindiga akalla 40 a yankin Birnin Magaji na jihar Zamfara.

Rundunar Sojin saman Najeriya ta ce hare-haren dakarunta a dajin sabon birnin dan Ali cikin karamar hukumar Birnin Magaji ya kashe ‘yan ta’adda 40, batagarin da wata majiya ke cewa suke aikata satar shanu a yankin.

Can a yankin Zurmi ma wani mazaunin garin Abdullahi Mamman ya ce harin Sojin ya kashe wani jagoran ‘yan bindigar Gwaska Dankarami.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories