‘Yan Najeriya miliyan 25 ke fama da tsananin yunwa – Bincike

0
49

Akalla ‘yan Najeriya miliyan 25 ne ke fama da yunwa, yayin da mutane miliyan 9.3 ke fama da matsanancin karancin abinci, dai-dai lokacin da kasar kef ama da tashen-tashen hankula na masu dauke da makamai.

A cewar Farfesa Kola Matthew Anigo, babban jami’in kula da harkokin ilimi da bincike kan bunkasa abinci mai gina jiki a Najeriya, kasar na cikin mawuyacin hali da ta bukatar agajin gaggawa.

Farfesan ya bayyana haka ne a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron shekara-shekara na kungiyar karo na 52.

Ya ce Najeriya ce ta daya a Afirka sannan ta biyu a duniya a jadawalin yara masu fama da cutar tamowa.

Anigo ya ce rashin tsaro da ake fama da shi a kasar yana yin babbar barazana ga Najeriya ta cimma burin samar da abinci mai gina jiki ga yara nan da shekarar 2025.

 

RFI