HomeLabaraiBabu wata takaddama a cikin jam'iyar mu - APC

Babu wata takaddama a cikin jam’iyar mu – APC

Date:

Related stories

INEC ta ayyana 29 ga Maris a matsayin ranar zaben cike gurbi a Adamawa

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta...

IPOB ta umarci ‘yan kabilar Igbo da ke Legas su koma gida

Kungiyar masu rajin kafa ‘yantacciyar kasar Biafara ta IPOB,...

Sarkin Kano ya taya Abba Kabir murnar lashe zaben gwamnan Kano

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya taya Abba Kabir...

Mata magoya bayan PDP na zanga-zangar kin amincewa da zabe a Kaduna

Wata tawagar mata sanye da bakaken kaya na jam’iyyar...

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi ƙarin haske game da cece-ku-cen da ake yi musamman a shafukan sada zumunta na internet kan jerin sunayen tawagar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da ta fitar.

Ƙananan maganganu sun fara ɓulla ne bayan da aka ga babu sunayen wasu jiga-jigan jam’iyyar a cikin jerin sunayen, ciki kuwa har da mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo – wani abu da masana ke ganin zai iya barin baya da ƙura.

Bala Ibrahim shi ne Daraktan yaɗa Labaran Jam’iyyar kuma ya shaida wa BBC cewa ba lalle bane a ga sunan kowa da kowa a cikin jerin sunayen mambobin kwamitin saboda “an kafa kwamiti ne domin taimakawa, kuma ba wai ana nufin mutum ɗaya shi zai iya komai ba, inda ka ji an ce mataimaki, akwai wani sama da shi,”

“A wannan kwamiti an duba an ga babu sunan shugaban ƙasa?, idan akwai shugaban ƙasa, maganar mataimaki ya shigo ba ta taso ba,” a cewar Bala Ibrahim.

Ya bayyana cewa tun bayan fitar da jerin sunayen, jam’iyyar ba ta yi wata ganawa a kan lamarin ba.

A cewarsa, an kafa kwamitin domin tsara dabarun neman ƙuri’ar ƴan Najeriya saboda akwai buƙatar waɗanda sunayensu ba sa cikin kwamitin su karkatar da kansu ga ayyuka masu muhimmanci.

Ya ce akwai yiwuwar a samu sauye-sauye a Jam’iyyar – “bayan wannan kwamitin, akwai wasu ƙananan kwamatoci da za a kafa na shiyya-shiyya, akwai wasu waɗanda ba lalle bane a ga sunansu ɓaro-ɓaro cikin kwamiti, amma rawar da suke takawa tana da yawa, wataƙila sune fitilar da ke haska wa wannan kwamiti hanya ya ga inda zai bi.”

BBCHAUSA

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories