HomeLabaraiGwamnati ta tafka asarar N280bn a kudaden shigarta na watan Agusta

Gwamnati ta tafka asarar N280bn a kudaden shigarta na watan Agusta

Date:

Related stories

Manyan kabilar Fulani suna so su ga bayana – Gwamna Ortom

Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya koka da cewa...

Kotu ta raba auren ‘yar Ganduje da shafe shekaru 16

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano...

Kotu ta aike da Murja Kunya zuwa gidan yari

Wata kotu a Kano ta aika da Murja Ibrahim...

Gwamnatin Tarayya ta ce kudaden shigar da take samu daga kamfanoni (CIT), da na ribar man fetur (PPT), da iskar Gas ya ragu matuka a watan Agusta, yayin da na kayayyaki (VAT),  da na shigo da kaya daga ketare, suka karu sosai.

Gwamnatin ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Kwamitin Kasafta Kudaden Asusun Tarayya (FAAC) ya fitar, bayan kammala taro a Abuja.

A cewar sanarwar, sabanin watan Yuli da gwamnatin ta raba N954.085bn tsakaninta da gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi, a Agusta jimillar N280.948bn kacal suka samu kasaftwa

Daga cikin wadannan kudaden ne a cewarsa, Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 256 domin gudanar da ayyukanta, yayin da jihohi 36 suka samu biliyan 222, Kananan Hukumomi kuma N164.247bn. sai jihohin da ake hako danyen man da suka samu biliyan 26.30.

Sanarwar dai na nuna jimlar kudaden shiga na VAT da ta samu ya kai Naira biliyan 215.266, wanda ya dara na watan Yuli., kuma  daga shi ne Gwamnatin Tarayya ta samu biliyan 32.290, jihohi kuma biliyan 107.633bn, sai kananan hukumomi N75.343bn.

Kwamitin ya kuma ce asusun adana kudaden shigar danyen man fetir a Agustan ya tsaya kan Dalar Amurka 470,599.54, wanda hakan ke nuna  ba a samu riba ko faduwa ba har zuwa watan Satumba, tun daga watan Yuli.

Sai dai an samu raguwarsa daga dala miliyan 35.37 a watan Mayu zuwa Dala 376,655 a watan Yuni, kafin ya kai Dala 470,599.54 a watan na Yuli.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories