HomeLabaraiSojoji sun kashe ‘yan ta’addan ISWAP da dama a Yobe

Sojoji sun kashe ‘yan ta’addan ISWAP da dama a Yobe

Date:

Related stories

Muna da buhunan sabbin takardun Naira — ’Yan bindiga

’Yan bindiga sun saki wani bidiyo suna ikirarin cewa...

‘Yan Najeriya sun jingine kasuwancin su a Nijar saboda karancin Naira

'Yan Najeriya da dama sun jingine harkokin kasuwancinsu a...

Gwamnatin Ribas ta soke amincewar amfani da filin wasanta wajen kamfen din Atiku

Gwamnatin jihar Ribas ta janye amincewarta na amfani da...

Babu wanda ya ke yakar Tinubu a fadar shugaban kasa, cewar gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ba...

Dakarun sojojin Nijeriya sun kai hari kan wani taron tattaunawa da kungiyar ‘yan ta’addar ISWAP ta shirya a tsakanin mambobinta, inda suka kashe ‘yan ta’addan da dama a jihar Yobe.

LEADERSHIP ta samu cewa ‘yan ta’addan sun hadu ne a wani wuri da ake kira Wulle a babura da motoci da nufin kai hari kan sansanin sojoji mafi kusa.

Wani rahoton leken asirin da Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi ya samu daga manyan majiyoyin soji, sannan LEADERSHIP ta samu, ya bayyana cewa, a bisa bayanan sirrin, sojojin bataliya ta 27, sun harba rokoki da dama kan ‘yan ta’addan wanda hakan ya yi sanadiyyar kashe ‘yan ta’addan da ba a tantance adadinsu ba.

An kuma bayyana cewa daga baya ‘yan ta’addan sun dawo a kan babura shida da mota daya domin kwashe gawarwakin mutanen su.

 

LEADERSHIP

 

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories