An yi jana’izar fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Umar Malumfashi

0
71

An yi jana’izar fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Umar Malumfashi, a jihar Kano.

Marigayin wanda aka fi sani da Ka fi gwamna a shirin Kwana Casa’in ya kwanta dama a daren ranar Talata, 27 ga watan Satumba.

Gomman jama’a ciki harda manyan abokan sana’ar marigayin sun samu halartan jana’izarsa wanda aka yi a safiyar yau Laraba.