Kasar Qatar da hukumar kwallon ta Duniya, FIFA sun samu matsaya akan haramcin shan giya.
Saidai kasancewarta kasar musulunci akwai abubuwa irinsu matan dake tafiya tsirara da giya da haramunne a aikata.
Amma akan maganar giya, hukumar FIFA ta shawo kan kasar Qatar inda ta amince a kurba a cikin filin wasan kamin wasa da bayan wasa.
Kamfanin Budweiser wanda shine ke daukar nauyin sayar da giya a gasar cin kofin Duniya shekara sa shekaru ne zai sayar da giyar a Qatar.