Kasar Qatar ta sassauta haramcin shan barasa saboda gasar cin kofin duniya

0
81

Kasar Qatar da hukumar kwallon ta Duniya, FIFA sun samu matsaya akan haramcin shan giya.

Qatar dai itace zata shirya gasar cin kofin Duniya na bana wanda kuma ta foke kasashe ciki hadda Amurka kamin ta samu wannan damar.

Saidai kasancewarta kasar musulunci akwai abubuwa irinsu matan dake tafiya tsirara da giya da haramunne a aikata.

Amma akan maganar giya, hukumar FIFA ta shawo kan kasar Qatar inda ta amince a kurba a cikin filin wasan kamin wasa da bayan wasa.

Kamfanin Budweiser wanda shine ke daukar nauyin sayar da giya a gasar cin kofin Duniya shekara sa shekaru ne zai sayar da giyar a Qatar.