Mutane fiye da 20 sun babbake kurmus yayin da wata tanka ta kama da wuta

0
41

Wata mota da ta dauko man fetur ta kife a gada da aka samu wani mummunan hadari.

Hadarin ya yi sanadiyyar dinbin mutane da-dama, wasu suna cewa akalla mutane 20 sun cika.

Abin ya auku ne a wata gada da ke garin Ankpa, jami’an FRSC sun tabbatar da lamarin.