Ina da yakinin Najeriya za ta iya shawo kan matsalolinta – IBB

0
50

Tsohon Shugaban Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya sake jaddada goyan bayan sa ga ci gaban kasar a daidai lokacin da take bikin cika shekaru 62 da samun yancin kai.

Yayin ganawa da manema labarai, Babangida yace kowacce kasa a duniya na da irin nata matsaloli, saboda haka yana da yakinin cewar Najeriya na iya shawo kan matsalolin da suka addabe ta a wannan lokaci domin habaka kamar sauran manya kasashen duniya.

Tsohon shugaban yace babu wata kasa a duniya da ta samu ci gaba kamar yadda kowa ke bukata, sai dai wasu sun fi wasu lura da yanayin su da kuma halin da suka samu kansu.

Babangida yace akwai wasu kasashen da suka kwashe shekaru sama dubu guda, amma har yanzu suna nan suna fafatawa domin ganin sun tsaya da kafafuwansu, inda yace haka Najeriya zata ci gaba da kokarin har zuwa lokacin da zata shawo kan matsalolin ta.

Dangane da zabe mai zuwa, tsohon shugaban ya gargadi talakawan Najeriya da kar su bari yan siyasa suyi amfani da su wajen tashin hankali domin biyan bukatar kansu.

Tsohon shugaban ya jinjinawa gwamnatin Najeriya akan matakan da take dauka wajen tinkarar matsalar tsaro, kuma yana da fatar ganin gwamnati ta samu nasara akai.

Babangida ya kuma janyo hankalin matasa da su kaucewa duk wasu yan siyasar dake neman amfani da su wajen rikicin kalibanci ko addini ko wani abinda zai raba kan jama’ar kasa.

Janar Babangida ya kuma bukaci Yan takaran zabe da su shaidawa Yan Najeriya kudirorin da suke da shi kafin zabe, domin baiwa jama’a damar sanin wanda yafi cancanta da kuma irin abinda ake tsammani a gare shi idan ya karbi mulki.