Mahaifiyar Babba Dan Agundi ta rasu 

0
59

Mahaifiyar Baffa Babba Dan Agundi, shugaban Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA), ta riga mu gidan gaskiya.

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar.

Sanarwar ta ce, “Innalillahi Wa Inna ilaihi rajiun.

“Hukumar Kula da Zirga-Zirga Ababen Hawa ta jiha KAROTA na sanar da al’umma rasuwar mahaifiyar Shugaban Hukumar Hon Baffa Babba Dan Agundi

“Ta rasu a jiya Lahadi da daddare sakamakon gajeriyar rashin lafiya.

“An yi jana’izar ta a yau Litinin da misalin karfe 10 na safe a gidan marigayi Sarkin Dawaki Babba da ke unguwar Dan Agundi.

“Muna addu’ar Allah ya jikanta da gafara ya sa ta huta ya ba mu hakurin jure rashin ta.