HomeLabarai’Yan bindiga sun sace mutum 7 a Sokoto

’Yan bindiga sun sace mutum 7 a Sokoto

Date:

Related stories

Sarkin Dutse Nuhu Sunusi ya rasu

Allah ya yi wa Sarkin Dutse Alhaji Dr. Nuhu...

Shin ko kunsan tsibirin da aka hana kowa zuwa a duniya ?

Shi wannan guri Mai suna North Sentinel Island an...

Mayakan ISWAP sun raba wa fasinjoji dubu dari-dari

Mayakan ISWAP sun rarraba wa fasinjoji da dama Naira...

Ya kamata mutane su yi amfani da kwanaki 10 wajen mayar da tsofaffin kudin su banki – Sanusi

Sarkin Kano murabus kuma Khalifan Tijaniyya, Sanusi Lamido Sanusi,...

‘Yan sanda sun bankado maboyar ‘yan bindiga, sun cafke mutum 6 a Nasarawa

Rundunar ‘yansandan Jihar Nasarawa ta ce ta kai farmaki...

‘Yan bindiga sun sace mutum bakwai yayin da suka kashe wasu mutum biyu a hare-haren baya bayan nan da suka kai Jihar Sokoto.

Dan Majalisar Dokokin Jihar Sokoto mai wakiltar mazabar Illela, Bello Isa Ambarura ne ya tabbatar da hakan.

Ya ce duk da yawan jami’an tsaro da ke kan hanyar Illela barayi na ci gaba da kai wa jama’ar yankin hare-hare.

Ya kara da cewa kwana biyu da suka wuce ’yan bindiga sun kai hari a wani gari mai suna Kalaba, inda suka sace mutane uku.

Bayan haka a ranar Alhamis maharan sun sake kai hari a wani gari da ke yankin Darna Tsaulawo, inda suka kashe mutum biyu suka kuma sace wasu biyar.

A baya, ’yan banga kan taimaka wajen tsaron jama’a amma yanzu abin ya fi karfinsu, duba da yadda barayin ke zuwa da yawa dauke da manyan makamai.

A kan batun rashin tsaro dai ‘yan Najeriya na ci gaba da zura ido su ga yadda Allah zai yi, domin matsalar ta ki karewa duk da kokarin da mahukunta ke cewa suna yi.

AMINIYA

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories