Gwamnan Oyo ya bawa masallatan Hausawa gudunmuwar motoci

0
71

Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya bayar da gudunmawar sabbin motocin bas guda biyu ga manyan masallatai biyu da ke Unguwar Sabo a birnin Ibadan.

Sarkin Musulmin Kasar Yarbawa da Jihohin Edo da Delta, Alhaji Dawud Akinola ne ya mika mabudan sababbin motocin ga manyan masallatan biyu na ’yan Darika da Izala.

Da yake mika motocin a madadin gwamnan, Alhaji Dawud Akinola ya ce wannan yana daya daga cikin alkawarin da gwamnan ya yi wa al’ummar Arewa mazauna Jihar Oyo ne.

Bayan karbar mabudan motocin, Limamin babbanmasallacin Sabo, Sheikh Sa’adu Abubakar ya fara yin addu’ar rokon Allah zaunar da Jihar Oyo da kasa baki daya lafiya, tare da jinjina wa Gwamna Seyi Makinde da yi masa fatan alheri a mulkin adalci da yake yi a jihar.

Shi kuwa Limamin babban masallacin (JIBWIS), Sheikh Sani Haruna cikin hudubarsa a wannan rana, ya nemi dukkan ’yan Arewa a wannan sashe su rika shiga cikin harkokin siyasa a wuraren da suke zaune domin a rika yin tafiyar tare da su kada a bar su baya.

Ya ce “mika kan da mutanenmu suka yi cikin wannan gwamnati ne ya kai ga samun wannan gudunmawar motoci.”

Da yake yi wa Aminiya karin haske, mai bai wa gwamnan shawara kan al’ummaran ’yan Arewa a Jihar Oyo, Alhaji Ahmad Murtala ya ce a gaskiya al’ummar Hausawa Musulmi sun yi matukar farin ciki da wannan gudunmawar motoci biyu da ya ce an sayi kowace guda daya a kan Naira miliyan 16.

Ya ce “idan ka tuna kwanan baya Hukumar Wutar Lantarki ta dakatar da raba hasken lantarki na tsawon wata hudu a Unguwar Sabo, a dalilin kasa biyan kudinsu, inda Gwamna Makinde ya taimaka ya biya Naira miliyan biyar daga cikin kudin kuma aka da dawo da hasken lantarkin.”

Ya yi kira ga ’yan Arewa da su kasance masu hakuri da girmama zamantakewar su da jama’ar gari, domin zama lafiya da kwanciyar hankali.

 

AMINIYA