Najeriya ta gaza kamo fursinoni 422 da suka tsere daga gidan yarin Kuje

0
52

Wasu bayanai na nuni da cewa watanni 4 bayan harin gidan yarin Kuje da ke garin Abuja fadar gwamnati har yanzu akwai fursunonin fiye da 400 da suka tsere kuma ba tare da hukumomin kasar sun iya nasarar kamo su don dawo da su gidan yarin ba.

Yayin harin na gidan yarin Kuje a ranar 5 ga watan Yulin shekarar da muke cike alkaluma sun nuna cewa akwai fursinoni akalla 879 da suka tsere ciki har da gagga-gaggan masu laifi da suka kunshi ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram 64.

Alkaluman baya-bayan nan da jaridar Punch ta wallafa sun nuna cewa, har zuwa yanzu mahukuntan Najeriyar basu iya kamo fursinonin 422 ba.

Mahukuntan gidan yarin sun sanar da kamo fursinoni akalla 32 cikin 454 da suka tsere daga watan Yuni zuwa yanzu a harin wanda kungiyar ISWAP ta yi ikirarin kaiwa.

RFI