Hadarin motar daukar mai ya hallaka mutum uku da kona motoci 12 a jihar Ogun

0
54

Mutum biyu sun mutu motoci 12 kuma suka kone lokacin da wata motar dakon man fetur ta kama da wuta a titin Lagos zuwa Abeaokuta a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Hadarin da ya faru a cikin daren da ya gabata wayewar garin yau Alhamis, ya kuma yi sanadiyyar raunata wasu mutum uku da suka tsira da kuna.

Mai magana da yawun hukumar kiyaye hadura a jihar ta Ogun Florence Okpe, ta ce motar dakon man tana hawa tudun Ilo Awele ne a wannan hanya lokacin da ta gangaro baya ta fadi da misalin karfe 1:30 na dare.

Daga nan kuma sai man da take dauke da shi ya rika zuba, sai ta kama da wuta.

Ta ce, an kilace wurin domin gudun kada lamarin ya rutsa da wasu motocin kuma tare da kiran ‘yan kwana-kwana,

Jami’ar da kara ta cewa zuwa karfe 4:05 na asuba gobarar ta rutsa da motoci 12, wadanda suka hada da manyan motocin safa uku da babur mai kafa uku guda hudu da babur uku da motar kiya-kiya daya sai kuma ita motar dakon man da ta haddasa wutar.

Ta kara da cewa an ceci mutum uku, wadanda suka hada da maza biyu da mace daya, wadanda aka kai su babban asibitin Ota.

BBCHAUSA