Sojoji sama da 60 za su gurfana gaban shari’a saboda take doka

0
49

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana shirin hukunta dakarun ta guda 68 saboda samun su da aikata laifuffuka daban daban, lokacin da runduna ta 8 dake Sokoto ke gudanar da rawan daji domin kakkabe ‘yan ta’adda a jihohin Sokoto da Zamfara da Kebbi da kuma Katsina.

Kwamandan Runduna ta 8, Manjo Janar Uwem Bassey dake dake kuma jagorancin Rundunar da ake kira ’Hadarin Daji’ ya bayyana haka lokacin da yake kaddamar da kotun da zata gudanar da shari’ar.

Janar Bassey wanda yayi suna wajen kutsa kai sansanonin ‘yan ta’adda yana kai musu hari, ya bukaci alkalan da za suyi shari’ar da su tabbatar da adalci dangane da zargin da ake yiwa sojojin.

Kwamandan yace lura da cewar wadanda zasu gurfana a gaban kotun sojoji ne kamar su, saboda haka suna bukatar girmamawa da kuma adalci.

Janar Bassey yayi alkawarin cewar kotun za tayi amfani da kundin tsarin mulkin shekarar 1999 wajen gudanar da shari’un dake gabanta.