An sace wayar namadi sambo a wurin kaddamar da littafi a Abuja

0
63

An sace wayar salular tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Arc. Namadi Sambo a wurin wani taro a babban birnin tarayya, Abuja.

Sanata Shehu, tsohon dan majalisar tarayya, wanda ya bayyana hakan a Twitter a ranar Alhamis, ya ce lamarin ya faru ne a wurin kaddamar da littafin “Chronicles Of The Rainbow”, tarihin marigayi Gwamna Solomon Lar.

Ya ce akwai jami’an tsaro sosai a wurin taron amma wani ya ‘kutsa’ ya sace wayar salulan.

Ya rubuta:

“Abin mamaki ne yadda wani ya tsallake matakan tsaro ya sace wayar tsohon mataimakin shugaban kasa Sambo a taron kaddamar da litafin marigayi Gwamna Solomon Lar a Abuja.”