Sojoji sun cafke ‘yan ta’adda 79 a jihar Borno

0
92

Dakarun Najeriya karkashin runduna ta musamman ta ‘Operation Hadin Kai’’, sun cafke ‘yan ta’adda akalla 79 tare da masu taimaka musu a yankin Arewa maso gabas cikin makwanni biyu da suka gabata.

Darakta mai kula da harkokin yada labarai na ma’aikatar tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami, ne ya bayyana hakan jiya Alhamis a Abuja, yayin taron manema labarai na mako biyu kan ayyukan rundunar.

Manjo Janar Danmadami ya kara da cewar sojojin Najeriyar sun kashe ‘yan ta’adda da dama, yayin farmakin da suka kaddamar akansu ta sama da kasa, tare da kubutar da mutane 14 da suka yi garkuwa da su, ciki har da ‘yan matan sakandiren Chibok biyu a tsawon makwanni biyun.

Danmadami ya bayyana sunan ‘yan matan da aka ceto da Yana Pogu da kuma Rejoice Senki tare da ‘ya’yansu da suka Haifa da mayakan na Boko haram wadanda suka sace su tun shekarar 2014.

Sojojin Najeriyar sun kai sumame ne kauyukan Bula Davo da Kawur a kananan hukumomin Bama da Konduga inda suka ceto ‘yan matan hade da wasu fararen hula 12, baya ga kame mayakan ISWAP 29 da kuma kayakin yaki, sai manyan buhunan bisasshen kifi 50 kana buhunan busasshen nama 2 sai jarkokin fetur 55 da tsabar kudi Naira miliyan 2 da dubu 400.

Haka zalika yayin sumamen Sojin Najeriyar sun kuma kame wani kwararre dake hada harsashin bindiga.