Ɗan majalisa Aminu Kuramu ya rasu a Saudiyya

0
57

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Bakori a majalisar dokokin jihar Katsina, Dr Ibrahim Aminu Kurami, ya rasu a Saudiya.

Dan majalisar ya tafi kasa mai tsarkin ne domin yin aikin Umrah.

A cewar wata majiya daga yan uwansa, ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya a Madina misalin ƙarfe 2 na dare lokacin Najeriya.

Ya rasu ya bar matan aure biyu, ƴaƴa 11 da jikoki guda uku. An zabi Kurami ne matsayin dan majalisa a Katsina a zaben raba gardama da aka yi a ranar 31 ga watan Oktoban 2020, bayan rasuwar magabacinsa, Hon. AbdulRazaq Ismail Tsiga.

A lokacin da Daily Trust ta ziyarci gidan iyalan Kurami a ranar Litinin da safe, ta tarar da dandazon mutane da suka taho ta’aziyya.