Gobara ta kama a majalisar dokokin Jihar Kogi

0
54

Majalisar Dokokin Jihar Kogi ta kama da wuta a safiyar wannan Litinin din.

Kawo yanzu dai ba a kai ga gano musababbin tashin gobarar ba.

Darektan Hukumar Kashe Gobara ta jihar, Salau Ozigi ne ya tabbatar da faruwar hakan, yana mai cewa gobarar ba ta tsallaka cikin farfajiyar zaauren majalisar ba.

Kakakin Majalisar, Prince Mathew Kolawole, ya alakanta faruwar gobarar da sakaci, yana mai cewa jami’an tsaro za su gudanar da bincike a kan lamarin.

Kazalika, ya ce wannan ibtila’i ba zai kawo wa majalisar wani koma baya ba wajen ci gaba da sauke nauyin da rataya a wuyanta.