HomeLabaraiMan fetur: Dogayen layuka sun dawo a gidajen mai a kano

Man fetur: Dogayen layuka sun dawo a gidajen mai a kano

Date:

Related stories

Sarkin Dutse Nuhu Sunusi ya rasu

Allah ya yi wa Sarkin Dutse Alhaji Dr. Nuhu...

Shin ko kunsan tsibirin da aka hana kowa zuwa a duniya ?

Shi wannan guri Mai suna North Sentinel Island an...

Mayakan ISWAP sun raba wa fasinjoji dubu dari-dari

Mayakan ISWAP sun rarraba wa fasinjoji da dama Naira...

Ya kamata mutane su yi amfani da kwanaki 10 wajen mayar da tsofaffin kudin su banki – Sanusi

Sarkin Kano murabus kuma Khalifan Tijaniyya, Sanusi Lamido Sanusi,...

‘Yan sanda sun bankado maboyar ‘yan bindiga, sun cafke mutum 6 a Nasarawa

Rundunar ‘yansandan Jihar Nasarawa ta ce ta kai farmaki...

Jaridar Aminya ta ruwaito Dogayen layukan mai sun sake dawowa a gidajen mai a Kano, tun a karshen mako saboda karancin man fetur, wanda daidaikun gidajen mai ke sayarwa a halin yanzu.

A yayin da gidajen da mansu ya kare suke a rufe, wasu masu shi tuni suka kara farashi, inda wasunsu ke sayar da lita a kan N220, wasu kuma sun rufe sun koma sayar wa masu bumburutu.A gidajen mai ’yan kalilan da ke da man kuma ba su kara farashi daga N185 ba, da kuma gidajen man NNPC da ke sayarwa a N185, masu ababen hawa sun yi cikar kwari domin samu.

Tuni dai fasinjoji suka fara kokawa, a yayin da wasu masu ababen hawa daga garin Kano kan fita zuwa gidajen man da ke kan hanyan kauyuka su shan mai.

Wani mai tuka babur din A-Daidaita-Sahu, Shuaibu Ibrahim, ya shaida wa Aminiya cewa ya shafe kimanin awa biyu a kan layi kafin ya samu mai.

“Har yanzu ba a kara farashi ba a gidajen man da na sha mai daga jiya zuwa yau (Litinin).

“Suna sayar da lita a kan N185 amma sai da na kai awa biyu kafin na samu, wanda hakan na shafar sana’armu, kuma fasinjojinmu ba za su fahimta ba idan aka yi musu karin kudi.”

Amma wasu masu ababen hawan sun ce sukan sha mai a cikin garin Kano, a kan sabon farashi da aka kara, kuma suka wuce minti 30 a kan layi.
“Jiya (Lahadi) na sha mai amma lita a kan N220, shi ma din sai da na yi tafiyar mai nisan wasu kilomitoci daga Jami’ar BUK, kuma sai da na bi layi.

“Ban san me ya faru ba, amma na lura akwai karancin mai kuma an kara farashinsa,” in ji wani mai abin hawa, Gambo Shuaibu, a hirarsa da wakilinmu.

Kasuwar ’yan bumburutu ta bude

Wannan yanayi ya sa tuni kakar ’yan bumburutu ta yanke saka, inda suke kara N50 a kan farashin kowace lita daya ta man fetur.

Wasu daga cikinsu sun bayyana wa Aminiya, “Mu ma sai mun bi layi a gidajen mai da tsakar dare muke samu, kuma sun yi mana karin kudi, saboda haka ba mu da zabi, dole sai mun kara farashi.”

Akwai wadataccen mai

Amma Zauren Dillalan Mai na Kasa ya ce Kamfanin NNPC na da isasshen mai da za a raba a yankin Arewacin Najeriya.
Sai dai ya bayyana cewa matsalar lalacewar hanya, musamman hanhar Lakwaja, sakamakon ambaliya ce ke kawo jinkiri wajen isowar man zuwa Arewa daga yankin Kudu.

Shugaban zauren, Alhaji Musa Y Maikifi ya ce, “Yanzu rashin kyan hanya ne matsalar, domin a yanzu direba kan kwashe kwana uku a tafiyar da ba ta wuci kilomita 70.

“Wannan shi ne ya haifar da wadannan matsaloli, amma ba mu kara farashi ba har yanzu.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories