Rasha da Belarus za su hada kai wajen yakar Ukraine

0
61

Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko ya ce kasarsa da Rasha za su tura rundunar hadin gwiwa ta soji domin mayar da martani ga abin da ya kira kara ta’azzara matsalolin da ke kan iyakokin yammacin kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Belta ya bayyana.

Lukashenko ya ce kasashen biyu sun fara hada karfi da karfe ne kwanaki biyu da suka gabata, bisa ga dukkan alamu bayan fashewar wani abu a wata gadar da ta hada Rasha da yankin Crimea da Rashan ta karbe a shekarar 2014.

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da makamai masu linzami na Rasha suka kai hari a garuruwa da dama a cikin Ukraine, ciki har da babban birnin kasar, Kyiv, a karon farko cikin watanni.

Ya kara da cewa, “Mun amince da tura rukunin dakaru na Tarayyar Rasha da Jamhuriyar Belarus.”

Sai dai Lukashenko bai bayyana inda za a tura sojojin ba.

Shugaban ya ce “dole ne Belarus ta kasance cikin shirin ko ta kwana, domi tunkarar duk wasu tsageru da ke kokarin jefa kasashen mu cikin rikici”.

Belarus ta fannin tattalin arziki da kuma siyasa, ta dogara ne akan babbar aminiyarta ta Rasha.

Dakarun Rasha sun yi amfani da kasar Belarus a matsayin matattarar farmakin da suka kai wa Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu, inda suka aike da sojoji da kayan aiki zuwa arewacin Ukraine daga sansanonin da ke Belarus.