Kalubale mafi muni na tunkarar tattalin arzikin duniya – IMF

0
69

Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya yi gargadin cewa duniya za ta kara fuskantar mafi munin kalubale, yayin da ake ci gaba da yaki a Ukraine da kuma fama da hauhawar farashin kayayyaki.

Kididdigar da IMF ya fitar na cewa, daga nan zuwa 2023 mutane da dama za sus amu koma bayan tattalin arziki.

Hukumar da ke aikin daidaita tattalin arzikin duniya, ta rage hasashen ci gaban tattalin arzikinta, sakamakon tasirin mamayar da Rasha ta yi a Ukraine.

Ana sa ran tattalin arzikin Birtaniya zai ragu a shekara mai zuwa, bayan da aka samu karuwar kusan kashi 0.3.

Wannan ya nuna raguwar kashi 0.2% daga hasashen IMF na Yuli, da faduwa daga kashi 3.6% na habakar tattalin arzikin Birtaniya da ake tsammanin samu a shekarar 2022.Asusun na IMF yana aiki don daidaita tattalin arzikin duniya kuma daya daga cikin manyan ayyukansa shine gaggawar tunkarar matsalolin da ke kokarin kawo tarnaki ga tattalin arziki.