Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 500 a Najeriya

0
42

Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da mutuwar akalla mutum 500 sanadin ambaliyar ruwan da take ci gaba da tafka barna a fadin kasar.

Mutanen sun mutu ne a makonni kadan da suka gabata.

Kazalika fiye da mutum 1,500 sun jikkata yayin da mutum miliyan daya da dubu dari hudu suka bar gidajensu sakamakon ambaliyar ruwan.

An fitar da wadannan alkaluman ne a wurin taron da hukumomin da ke da ruwa da tsaki kan sha’anin yanayi suna gudanar ranar Talata a Abuja, babban birnin kasar.

Taron, wanda Ministan harkokin noma ya jagoranta, ya kara da cewa baya ga mutuwa, ambaliyar ruwan ta kuma yi sanadin rushewar gida 45,249.

Kazalika hukumomin sun ce ambaliyar ruwan ta lalata hekta 70,566 na gonaki a fadin kasar, tana mai gargadin cewa akwai yiwuwar matsalar za ta ta’azzara.

‘Yan kasar dai suna ci gaba da kokawa game da yadda ambaliyar ruwan ta raba su da muhallansu inda a yanzu suke kwana a gine-ginen makarantu da sansanonin ‘yan gudun hijira.