Buhari ya rantsar da Ariwoola a matsayin babban alkalin kasa

0
56

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya rantsar da mai shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin babban alkalin alkalan Najeriya.

An gudanar da bikin rantsuwar ne jim kadan gabanin fara taron majalisar zartarwa ta tarayya na wannan mako.

Wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, da gwamnoni Seyi Makinde da Rotimi Akeredolu na jihohin Oyo da Ondo.

Wadanda suka halarci bikin sun hada da wasu alkalan kotun koli; Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya).

Sabon babban alkalin ya kuma yi alkawarin yin gyara a kotun koli da dama kamar saurin tabbatar da adalci da jin dadi da walwalar jami’an shari’a.