HomeLabaraiSojoji sun kashe ‘yan ta’addar ISWAP 19 a wata arangama a Borno

Sojoji sun kashe ‘yan ta’addar ISWAP 19 a wata arangama a Borno

Date:

Related stories

INEC ta ayyana 29 ga Maris a matsayin ranar zaben cike gurbi a Adamawa

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta...

IPOB ta umarci ‘yan kabilar Igbo da ke Legas su koma gida

Kungiyar masu rajin kafa ‘yantacciyar kasar Biafara ta IPOB,...

Sarkin Kano ya taya Abba Kabir murnar lashe zaben gwamnan Kano

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya taya Abba Kabir...

Mata magoya bayan PDP na zanga-zangar kin amincewa da zabe a Kaduna

Wata tawagar mata sanye da bakaken kaya na jam’iyyar...

Akalla ‘yan ta’addar ISWAP 19 ne suka rasa rayukansu a lokacin da dakarun Operation HADIN KAI suka fatattakie su a Gamboru Ngala da ke karamar hukumar Ngala a Jihar Borno.

Gamboru, wani gari ne mai iyaka da ke nisan kusan kilomita 128 zuwa Maiduguri, babban birnin jihar.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa sojojin tare da wata rundunar hadin gwiwa ta Civilian Joint Task Force (CJTF) sun cimma wannan nasara ne a ranar Talata, 11 ga watan Oktoba, 2022 bayan da suka dakile wani harin kwantan bauna da ‘yan ta’addan suka kai wa sojojin.

Wani rahoton leken asirin da Zagazola Makama, kwararre kan yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi ya samu daga manyan majiyoyin soji, wanda wakilinmu ya nakalto, ya bayyana cewa ‘yan ta’addan da suka zo da adadi mai yawa a kan babura da mota kirar Hilux dauke da bindigu, sun fara kai harin kan sojojin.

Majiyoyin leken asirin sun ce dakarun da ke da karfin gwiwa sun yi musu kwantan bauna wanda ya haifar da kazamin fadan da ya dauki tsawon mintuna 40 ana yi.

Ya ce daga baya sojojin sun mamaye ‘yan ta’addan da karfin wuta wanda hakan ya sa suka tsere.

Ya ce daga baya sojojin sun mamaye ‘yan ta’addan da karfin wuta wanda hakan ya sa suka tsere.

“Sojojin dai sun fatattaki ‘yan ta’addan da suka koma baya tare da kashe 19 daga cikinsu.

“Sojojin sun yi nasarar kama wata mota dauke da bindigu tasu bayan sun kashe dukkan mutanen da ke cikinta, sun kwato babura tara da kuma makamai da dama da suka hada da PKT daya, AK-47 guda tara da harsashi da dama.

“Ba a samu asarar rai ba a bangaren sojojin saboda biyu ne kawai suka samu rauni a bangarenmu,” in ji wata majiya.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa sojoji da rundunar hadin gwiwa sun samu nasarar ne biyo bayan bayanan sirri da suka samu a garin Gamborun Ngala.

 

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories