Zamfara ta sake bude makarantu 45 sakamakon samun tsaro

0
43

Gwamnatin jihar Zamfara ta bude makarantu 45 daga cikin 75 da ta rufe saboda rashin tsaro, kamar yadda ma’aikatar ilimi ta sanar a ranar Laraba a Gusau.

Sakataren dindindin a ma’aikatar, Alhaji Kabiru Attahiru ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin ‘yan kungiyar fasaha ta jihar kan harkokin ilimi a cikin gaggawa wadanda suka kai ziyarar neman shawara a ma’aikatar.

Gwamnatin jihar ta bayar da umarnin rufe makarantun ne a watan Satumban 2021 bayan sace daliban makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kaya a karamar hukumar Maradun.

“Yayin da muka sake bude makarantun, mun kasasu kashi uku – kore shudi dakuma ja. “kore sun kasance makarantu a wuraren da ba tare da barazanar tsaro ba, kungiyar shudi kuma na makarantun da ke yankunan da ke da ƙananan barazanar rashin tsaro, yayin da ja suka kasance makarantu a yankunan da ke da hadarin tsaro,” in ji Attahiru.

Ya ce dukkan makarantun 75 sun fada cikin kungiyar ja a lokacin da aka rufe su saboda yana da hadari a bar su a bude.

“A yau, ina mai farin cikin sanar da ku cewa, sakamakon inganta tsaro a jihar, mun bude makarantu 45 daga cikin 75, yayin da makarantu 30 kacal suka rage a rufe.

“Gwamnati da hukumomin tsaro sun yi aiki tare domin tabbatar da ingantaccen tsaro a jihar.

“Muna fatan za a kara inganta harkokin tsaro a jihar domin mu sake bude sauran makarantu 30,”

PUNCH