Gwamnatin Kogi ta baiwa Dangote wa’adin sa’o’i 48 ya kulle kamfanin simintinsa

0
55

Baraka tsakanin gwamnatin Jihar Kogi da ke Najeriya da kamfanin simintin Dangote na dada zafafa sakamakon umarnin da Gwamna Yahya Bello ya bayar na rufe kamfanin a cikin sa’oi 48.

Jaridar Daily Najeriyan ta hannun kwamishinan yada labarai Kingsley Fanwo ta ruwaito cewar Gwamna Bello ya bukaci kamfanin Dangote da ya mutunta matsayin da Majallisar dokokin jihar ta dauka na bada umurnin rufe kamfanin har zuwa lokacin da Dangote zai gabatar mata da bayanan da ta nema daga hannunsa dangane da mallakar kamfanin siminiti Obajana da filayen dake wurin.

Bello ya ce a matsayinsu na hukuma za su kare matakan da gwamnati ke dauka daga kama karya, yayinda ya jaddadawa jama’ar jihar aniyarsa ta kare muradunsu ba tare da saba ka’ida ba.

Sanarwar kwamishinan ta ce ganin yadda gwamnan ke da goyan bayan mutanen jihar Kogi miliyan 4, zai ci gaba da daukar dukmatakan da suka dace wajen kare muradun su ta hanyar tanade tanaden dimokiradiya.

Kwamishinan ya bukaci jama’ar jihar da su kaucewa daukar doka a hannu domin baiwa hukumomi damar daukan matakan da suka dace.

A karshe gwamnan ya bada umurnin sakin manyan motocin Dangote da aka kama a sassan jihar sakamakon takaddamar da akeyi, yayin da ya bukaci jama’ar jihar da su tabbatar da ganin jihar ta dore a matsayin mai karbar bakin da ke bukatar zuba jari kamar yadda aka gani a shekaru 7 da suka gabata.