Nijar za ta fara fitar da gangar mai dubu 20 kowacce rana daga 2026

0
51

Yanzu haka aikin gina bututun mai mafi girma a Afirka ya kankama a Jamhuriyar Nijar, inda ma’aikata Yan kasar China da Najeriya ke taka rawa wajen ganin an shimfida bututun, yayin da jami’an soji ke basu kariyar da suke bukata.

Daga yankin Gaya dake kudu maso yammacin Nijar, kusa da Jamhuriyar Benin, aikin shimfida bututun man ya kankama wanda zai ci kilomita dubu 2, tare da ratsa kilomita dubu 1 da 250 a cikin kasar Nijar domin ganin ya hade da rijiyar man Agadem dake gabashin kasar, inda ake fama da matsalar Yan ta’adda har zuwa gabar ruwan Seme dake Jamhuriyar Benin.

Jamhuriyar Nijar dake samar da ganga dubu 20 na danyan man fetir kowacce rana, na daya daga cikin kasashen Afirka da suka fara aikin fitar da man a shekarar 2011 zuwa kasuwanni duniya.

Kamfanin man kasar China na CNPC ya fara aikin hako man wanda ake kai shi Zinder inda ake tace shi.

Tun farko Nijar ta shirya fitar da danyen man ta ta tashar ruwan Kribia dake kasar Kamaru, ta bututun da ake saran shimfida shi ta kasar Chadi, kafin daga bisani ta sauya shirin wanda ya koma ta Jamhuriyar Benin.

An dai kaddamar da wannan aiki ne a shekarar 2019 domin kammala shi a shekarar 2022, amma sai annobar korona ta dakatar da aikin kamar yadda mataimakin manajan kamfanin WAPCO Nafiou Issaka ya bayyana.

Shidai kamfanin WAPCO wani reshe ne na kamfanin man kasar China, kuma yanzu haka ya shimfida kilomita 600 na bututun man, wanda shine kashi 51 na aikin, abinda ake ganin Nijar zata fara sayar da man ta a kasuwannin duniya a watan Yulin shekara mai zuwa, kamar yadda ma’aikatar man kasar ta sanar.

Sama da sojoji 700 aka girke domin samar da tsaro ga ma’aikatan dake aikin shimfida bututun man.

Sakamakon faduwar farashin uranium a kasuwannin duniya, wanda Nijar ke da arzikin sa, gwamnatin kasar na sanya ido akan bangaren man fetur domin samun kudade dan aiwatar da kasafin kudin kasar, wanda akasarin sa ake karkatawa zuwa sayen kayen yaki da yan ta’adda.

Ana saran zuba jarin dala biliyan 6 a cikin wannan aikin, kuma biliyan 4 daga cikin su zai karkata ne zuwa wajen aikin rijiyoyin man dake Agadem, yayin da dala biliyan 2 da miliyan 300 za’ayi amfani da su wajen shimfida bututun.