Za a yi gwanjon kwallon da Diego Maradona ya ci a 1986

0
59

Za ayi gwanjon kwallon da Diego Maradona ya yi amfani da ita wajen zura kwallaye biyu da suka kafa tarihi a duniyar kwallon kafa.

Kwallon da aka yi amfani da ita a wasan daf da na kusa da karshe na gasar cin kofin duniya a shekarar 1986 tsakanin Ingila da Argentina na dauke da kimanin farashin sama da Yuro miliyan uku.

An yi amfani da kwallon ne tsawon mintuna 90 na wasan, wanda ya kasance daya daga cikin fafatawar da aka fi sani da ke cike da fasahohi a tarihin gasar cin kofin duniya.

Argentina ta ci wasan da ci 2-1 daga karshe kuma ta lashe gasar cin kofin duniya a Mexico.

Za a sayar da kwallon ne a ranar 16 ga watan Nuwamba a matsayin wani shiri na musamman na gasar cin kofin duniya. kuma ga duk wanda ke sha’awar siyen wanna kwallo zai yi rijista a ranar 28 ga watan Nuwamba.